Saturday 31 January 2026 - 19:29
Asali da Falsafar Wanzuwar Makarantun Hauza Na Da Nasaba da Mahadawiyya da Intizar

Hauza/ Shugaban makarantun Hauza na ƙasa, Ayatullah Alireza A'arafi, yayin jaddada cewa asali da falsafar wanzuwar makarantun Hauza ta ta'allaka ne akan haɗin kai mai zurfi da Mahadawiyya da Intizar, ya ce: Wannan alaka ce ta asali wadda ta bambanta makarantun Hauza da sauran cibiyoyin ilimi da na addini a duniya, kuma ta ɗora wani babban nauyi na tarihi a kan ɗalibai da masana makarantar kan ci gaba da tafarkin gina wayewar addinin Musulunci."

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, shugaban makarantun Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi ya yi maganar ne yayin bikin rufe gasar ilimi karo na tara na makarantun Hauza da aka gudanar a Cibiyar "Mataimakan Mahdi" da ke birnin Qum. Da yake magana akan matsayin makarantun Hauzar Qom a tarihi da wayewar ƙasa, Ayatullah A'arafi ya jaddada cewa: "Asali da falsafar wanzuwar makarantun Hauza ta ta'allaka ne akan haɗin kai mai zurfi da imani da Mahadawiyya kuma Intizar. Kuma wannan alakar ce ta bambanta makarantunmu da sauran cibiyoyin ilimi da na addini a duniya."

Shugaban makarantun Hauza na ƙasa, da yake girmama watan Sha'aban da kuma fuskantar watan Ramadan, ya ɗauki wadannan watanni biyu a matsayin "wata dama da ba za a iya misaltawa ba don tafiya zuwa ga Allah da kuma shiryawa don haɓaka ruhaniya." Ya kara da cewa: "Watan Sha'aban shi ne matakin kaiwa zuwa ga kololuwar ruhaniya, yayin da watan Ramadan kuma watan riba ne da haɓaka musamman ga ɗalibai da malamai na makarantun addini."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha